
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Ifeanyi Okowa da ya koma jam’iyyar APC daga PDP yace ba tsoron EFCC ne yasashi komawa APC ba.
A baya dai Hukumar EFCC ta fara binciken Okowa akan zargin batan Naira Tiriliyan 1.3 wanda daga baya kuma sai gashi ya koma jam’iyya me mulki ta APC.
Hakana a baya tsohon shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya taba fadar cewa duk dan siyasar da ya shiga APC an yafe laifinsa.
Wannan yasa mutane ke tunanin cewa dalili kenan da Okowa ya koma APC, amma ya musata hakan.
Ya kara da cewa, zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarat 2027 shine zai sa kasanan ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa.