
Bayan Shafe Tsawon Lokaci Suna Soyayya Daga Ƙarshe Dai Ana Raɗe-raɗin Mawaƙi Hamisu Breaker Ya Auri Jaruma Hafsat Idris
Shahararren mawaƙin nan na masana’antar Kannywood, Hamisu Breaker ya auri jaruma Hafsat Idris (Ɓarauniya) bayan shafe tsawon lokaci suna soyayya a sirrance.
Wasu rahotanni su bayyana cewa an ɗaura auren ne a makon da ya gabata. Idan ta tabbata, za a iya cewa ma’auratan sun shiga layin jaruman Kannywood da ke yin aure cikin sirri a baya-bayan nan.
Wane fata zaku yi musu?