Monday, December 16
Shadow

Remi Tinubu da Ribadu za su jagoranci yi wa Najeriya addu’a dan ta fita daga matsalar tsananin Rayuwa

Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci addu’a ta musamman domin neman sauƙin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Za a gudanar da addu’ar ne ƙarƙashin jagorancin jagororin addinin Musulunci da Kirista, domin neman taimakon Allah a kan ƙalubalen da suka yi ƙasar dabaibayi.

Chief Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu’ar ta ƙasa ne ya sanar da hakan a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce akwai buƙatar kowa ya bayar da nasa gudunmuwar domin magance matsalar da ƙasar ke fuskanta, inda ya nanata cewa haɗin kai na da muhimmanci wajen shawo kan dukkan matsala.

Karanta Wannan  Kasar Nijar ta koro 'yan Najeriya 148 da suka shigar mata kasa ba bisa ka'ida ba

“Bayan addu’ar, muna da yaƙinin Allah zai buɗe mana hanyoyin da za mu samu sauƙi,” Afolorunikan, inda ya ƙara da cewa Najeriya za ta shiga shekarar 2025 cikin walwala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *