Tuesday, January 14
Shadow

Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya janyo ambaliya a Makka

Matsanancin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan ƙasar Saudiyya.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye hanyoyi a cikin garin Makka.

Haka kuma an ga yadda wasu maza suka riƙe da hannu domin ceto yaran da suka maƙale sanadin ambliyar ruwan a unguwar Al-Awali.

Sai da aka soke jigilar wasu jiragen sama a birnin Jeddah, inda aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya janyo hukumomin Saudiyya suka rufe makarantu a daukacin ƙasar.

Karanta Wannan  IKON ALLAH: Ya Yi Gaŕķuwa Da Yaro Dan Shekara Bìýu, Inda Ya Nemi A Ba Shi Naira Milyan Hamsin Kùďin Fansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *