Friday, December 5
Shadow

Sabbin Bayanai sun sake fitowa game da sojojin da ake zargin sun yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Sabbin Bayanai sun sake fitowa game da sojojin da ake zargin sun yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Juyin mulki.

Kafar Premium times ta bayyana cewa, a cikin sojojin guda 16 da ake tsare dasu akwai Brigadier General daya da Conel daya da Lieutenant Colonel guda 4, sai masu mukamin Major 5 sai masu mukamin Captain 2, sai mai mukamin Lieutenant daya.

Guda 14 daga cikinsu sojojin kasa ne sai sauran akwai sojan ruwa dana sama.

Saidai har yanzu jaridar bata bayyana sunayensu ba.

Wata majiya dai tace an kama karin sojoji da ake zargi da hannu a lamarin bayan su.

Karanta Wannan  ALLAHU AKBAR: Yau Marigayi Sheik Abubakar Gero Argungu Ke Cika Shekara Guda Cif Da Rasuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *