Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta bayyana cewa an samu hadarin jirgin kasan dalilin satar karafan dake rike titin jirgin.
Hakan ya haddasa aka dakatar da jigilar jirgin ranar Alhamis na dan wani lokaci dan cire jirgin da ya samu matsalar.
Saidai me magana da yawun hukumar, Yakub Mahmood ya bayyana cewa duk wanda ya riga ya sayi tikitin jirgin, zai iya amfani dashi har nan da zuwa sati biyu masu zuwa.