
Dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa, Hon. Ibrahim Usman Auyo ya yi zargin cewa sai sun biya tsakanin Naira Miliyan 1 zuwa 3 sannan ake yadda su gabatar da kudirin doka a majalisar tarayya har a karantashi a zauren majalisar.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Ya kara da cewa, bayan haka sai mutum ya bi ‘yan majalisar yana rokonsu akan su goyi bayan kudirin nasa.
Yace dan haka maganar gabatar da kudirin doka a majalisar ya zama hanyar samun kudi.