Sunday, July 19
Shadow

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na bana

Ɗan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na kakar bana.

Wannan ne karo na biyu da Salah ya lashe kyautar, wanda ake yi bayan haɗa kuri’un jama’a da na masana harkar kwallon kafa – ɗan wasan ya taɓa lashe kyautar a kakar 2017-2018.

Salah wanda ya jagoranci ƙungiyarsa wajen lashe gasar Premier, ya doke abokan takararsa da suka haɗa da Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch da kuma Declan Rice.

Sauran waɗanda ya doke a lashe kyautar sun kunshi Alexander Isak da Bryan Mbeumo da kuma Chris Wood.

Wannan ne karo na farko tun kakar 2018-2019 da ɗan wasan Manchester City bai lashe kyautar ba.

Karanta Wannan  Daga yanzu karku kara yadda, Duk wanda aka yi Gharkiwa dashi ya biya kudin Fhansa ya kai Gwamnati kara ta biyashi kudinsa>>Inji Lauya Femi Falana

Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Masar ya zura kwallaye 28 da kuma bayar da 18 aka ci a wannan kakar da ke daf da karewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *