Wednesday, April 8
Shadow

Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Sanata Orji Uzor Kalu dake wakiltar mazabar Abia North a majalisar Dattijai ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa ne da manyan ma’aikatan Gwamnati da ‘yan Kasuwa ke daukar nauyin ayyuka Kungiyar Bòkò Hàràm.

Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV.

Yace kuma masu yin hakan suna yi ne dan kawai su hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu iya gudanar da Gwamnatinsa yanda ya kamata.

Yace amma ba ta haka bane ake karbar mulki, yace yawanci suna yi ne dan su kwace mulki daga hannun Tinubu ba kudi bane a gabansu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Wallahi Wanda suka Kawo Davido Kano basu Birgeni ba, da dai Limamin Harami suka kawo da shine zasu Burge>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *