Thursday, June 5
Shadow

Saudiyya: Matan wani dattijo mai shekaru 70 sun samar masa mata mai ƙarancin shekaru ya aura

Wani dattijo mai shekaru 70 a duniya, Awad Al-Thouaib, wanda ke da mata biyu, ya samu shawarar su da ya karo aure.

Al-Thouaib, dan garin Taif a kasar Saudiyya, ya karade kafafen watsa labarai bayan da ya sanar da cewa matan nasa sun bashi shawarar ya auri mata ta uku, har ma su ka ce ya nemi zuƙeƙiyar yarinya mai karancin shekaru ya aura.

A cewar sa, matan nasa sun mishi alkawarin biya masana kuɗin da zai dauki amaryar ta sa su je hutun angwanci a duk inda ya ke so.

Ya ce su ma matan nasa biyun sun fara tsufa, shi ne su ka bashi shawarar da ya nemo yarinya sabon jini yadda za ta tallafawa rayuwar sa.

Karanta Wannan  An kama mutane 2 da yiwa yarinya me shekaru 12 fyàd a jihar Yobe

Shafin Lifeinsaudia.com ya ruwaito cewa tuni matan biyu sun yi shirin biki na mijin nasu da duk wacce ya ga ta yi masa a matsayin mata ta uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *