Friday, December 5
Shadow

Sha’aban Sharada ya sauya sheƙa zuwa APC

YANZU-YANZU: Sha’aban Sharada ya sauya sheƙa zuwa APC

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADP a zaben 2023, Sha’aban Sharada ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar zuwa APC.

A wani faifen bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Sharada, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kano Municipal, ya sanar da komawa APC din ne a wata liyafa da ya haɗa ga magoya bayan sa a gidan sa da ke Kano.

Ya ce ya auna ya ga cewa “da sabon gini gwanda yaɓe”, bayan ya maida al’amuran ss ga Allah kan Ya yi masa zaɓi na alheri.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a kwanakin bayan an hango Sharada tare da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje a Abuja, lamarin da tun a lokacin ake kallon kamar yunkurin komawa jam’iyyar ta sa ya ke yi.

Karanta Wannan  Kaso 85 na wadanda muke daukar nauyinsu mu aikasu karatu kasashen Turawa basa dawowa dan su taimaka a gina kasarnan>>Gwamnatin Tarayya ta koka

A lokacin da ya ke takarar gwamna a Kano, a guraren kamfe da dama, Sha’aban Sharada ya caccaki Ganduje da jam’iyyar APC da ma ɗan takarar ta, Nasiru Yusuf Gawuna3, inda ya zarge su da cin hanci da wawure kuɗaɗen al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *