Wednesday, January 15
Shadow

Shagwaba a soyayya

Shagwaba gishiri ce ta soyayya wadda idan akwaita, masoyinki zai rika kara sonki kamar ba gobe.

Dolene ki iya narkewa da fadar kalamai cikin sanyin murya da iya fari da ido da dai sauransu dan kara dasa soyayyarki a cikin zuciyar masoyinki.

Shagwaba nasa ko da ku biyu ne ko kumama kunfi haka yawa a wajan masoyinki ya ji ya fi sonki fiye da sauran.

Kuma kar ki yi tunanin bai so, ko da da fari ya nuna rashin kulawa, ki ci gaba, kinsan wani miskili ne ba lallai kai tsaye ya fada miki cewa yana jin dadin shagwabar da kike masa ba.

Karanta Wannan  Abubuwan dake kara dankon soyayya

Idan ya zamana baki mai shagwaba, wata na masa, to in ba sa’a ba, waccan dake masa shagwabar zata kwaceshi ko kuma yafi karkata a bangarenta.

Abubuwan da zaki iya yi na shagwaba sun hada da:

Fari da ido.

Yauki yayin tafiya.

Sanyaya murya.

Murguda baki, bana rashin kunya ba.

Yin shiru amma kar yayi tsawo.

Da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *