Wednesday, January 15
Shadow

Shahararren Dan Ťa’àďdar Nan Da Ya Addabi Ýankunan ‘Yar Tashar Sahabi, Hanyar Dansadau Zuwa Magami Ya Bakunci Ĺahira, A Daidai Lokacin Da Ya Hadu Da Fushin Wasu Fusatattun Jaruman ‘Yan Sakai

Daga Imam Murtadha Gusau

Wasu jajirtaccin matasa ‘yan sakai wadanda suka sadaukar da rayuwar su tare da lokacin su, wurin kariyar al’ummah, sune suka farmaki Kacallah Black tare da tawagar yaran shi, a daidai lokacin da suka samu labarin cewa shararren dan ta’adda Black ya fito zai je wurin wata aika-aika, an samu nasarar kashe Black da yaran shi akalla kusan su 10, a wani yanki na dajin mai tashi dake yamma ga ‘Yar Tashar Sahabi dake kan hanyar Dansadau, an samu nasarar kwato mashuna da bindigogi tare da alburusai na wannan dan ta’addar da na yaran shi.

Rahotannin da suke zo muna daga mazauna yankin ‘Yar Tashar Sahabi, suna nuni da cewa wannan gagarumar nasara ce aka samu domin wannan dan ta’addar shine ya addabi yankin hanyar Dansadau zuwa Magami da kuma wasu bangarora na yankunan.

Karanta Wannan  Hotuna: 'Yan Bindiga sun kashe babban soja da bai dade da yin aure ba da sauran sojoji 3 a Sokoto

Sakamakon wannan gagarumar nasarar da aka samu, hakan yasa al’ummar garin ‘Yar Tashar Sahabi da suke kan hanyar Dansadau, suke ta murna da farin ciki tare da godiya ga Allah akan wannan gagarumar nasarar da aka samu, ta kashe wannan babban dan ta’adda.

Muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala, tare da fatan Allah yaci gaba da bayar da nasara akan wadannan aźźaĺumai, amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *