Friday, January 23
Shadow

Shekarar mu daya cur bamu ci nama ko kifi ba, babu abinci me gida jiki babu kulawar Lafiya>>Inji Masu Laifi dake daure a gidan gyara hali

Masu Laifi dake daure a gidan gyara hali na garin Jos a jihar Filato sun koka da cewa, yanayin da suke ciki ya munana.

A wani rahoto da kafar Sahara reporters ta wallafa, mai laifin sunce shekara daya kenan rabonsu da cin nama ko kifi, sai wake wanda babu wani abun gina jiki a cikinsa.

Hakanan sun koka da cewa, idan basu da lafiya babu kulawa kuma ana azabtar dashi ga nuna kabilanci.

A wani hoto da aka wallafa, an ga kalar abincin da ake baiwa masu laifin wanda ya hada da wake da garin rogo da miyar Kuka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Bazawara wadda tace ita Haryjace na neman Mijin aure da gaggawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *