Shugaban kamfanin Rukunin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa,shekaru 18 da suka gabata,Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu yana da burin gina matatar man fetur a Legas.
Yace amma sai gashi shi ya samu damar ginawa.
Yace burinsa shine, ya saka Afrika da Najeriya Alfahari.
Yace dalilin kujiba-Kujibar gina matatar man fetur dinsa gashi duk yayi farin gashi.
Yace a baya bashi da farin gashi amma yana alfahari da samunsa.