Thursday, October 3
Shadow

Amfanin rigar nono ga budurwa

Akwai amfani da yawa ga budurwa ta rika saka rigar nono. A wannan rubutu, zamu bayyana wadannan amfani.

Na 1. Rigar Nono na hana zubewar nono: Nono yakan tsaya da kansa ko da ba’a tareshi ba amma yana da kyau budurwa ta rika saka rigar nono dan yana taimakawa wajan hana zubewar nonon. A wani kaulin, an fi son budurwa ta saka rigar nono yayin da take aikin jijjiga jiki,amma a yayin da take zaune bata aikin komai, zai fi kyau kada ta saka rigar nonon.

Na 2. Rigar Nono na taimakawa budurwa wajan jin dadin jikinta da kuma bayyanar surarta da kyau. Musamman mata masu girman nono,Rigar Nono zata taimaka musu sosai wajan tsaida nonuwan yanda ya kamata.

Karanta Wannan  Gyaran nono lokacin yaye

Na 3. Yana karawa mace jin dadin jikinta da Alfahari da kanta. Mace zata samu nutsuwa sosai idan ta saka rigar nono.

Na 4. Kare mutunci: Saka rigar mama yana taimakawa mata su rufe nononsu da kyau, musamman kan nononsu wanda hakan zai taimaka wajan tsare mutuncinsu.

Na. 5. Rigar mama tana zama a matsayin abin gayu ga mata inda zaka ga ana da rigar nono kala-kala wadda mata kanso su saya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *