
Shirin jam’iyyun Adawa na hadewa waje daya dan yin galaba akan jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027 ya fara saun tangarda saboda komawa jam’iyyar APC me mulki da ‘yan Adawa dayawa ke yi.
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ke jagorantar wannan tafiya ta ‘yan adawa.
Duk da kokawar da ‘yan Najeriya ke yi na tsadar rayuwa amma jam’iyyar APC me mulki sai kara samun manyan ‘yan Adawa take suna komawa cikin ta.
A baya dai an yi tsamanin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC zasu sha wahala wajan cin zabe Wanda su kansu ‘yan Adawar abinda suka yi amfani dashi kenan wajv fara wannan tafiya tasu amma gashi lamarin na son dagule musu.