
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Abuja a yau, Juma’a dan zuwa kasashen Japan da Brazil ziyara.
Shugaban zai tsaya a Dubai, UAE kamin ya ci gaba da tafiyar tasa.
Shugaba Tinubu ya tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 11:15 na safiyar yau.
Manyan jami’an gwamnati da suka hada da shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati, Femi Gbajabiamila, da babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Ministan kudi, Wale Edun sun halarci filin jirgin.