
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a janye jami’an ‘yansanda dake baiwa manyan mutane tsaro a fadin Najeriya.
Shugaban yace duk wani babban mutum dake neman jami’an tsaro a bashi jami’an Civil Defence.
Shugaban ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda jami’an ‘yansandan dake a ofisoshin ‘yansanda dake Fadin Najeriya sun yi kadan.
Hakanan yace duk ‘yansandan za’a mayar dasu wajan aikin da shine dama ya kamata suna yi.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan taron da shugaba Tinubu yayi da shuwagabannin jami’an tsaro na kasa ranar Lahadi.
Sannan yace shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a dauki sabbin jami’an ‘yansanda guda dubu 30.