Sunday, September 27
Shadow

Shugaba Tinubu ya sake daga ranar dawowarsa Najeriya

A karo na biyu, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake daga ranar da zai dawo Najeriya.

A baya dai ranar Litinin data gabata ne shugaban zai dawo Najeriya bayan da hutunsa ya kare

Inda aka daga zuwa karshen sati watau yau Lahadi.

Saidai a yau ma Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya sake daga ranar dawowar tasa ba zai dawo yau ba.

Jaridar The Cable tace a yanzu shugaban kasar ya sake saka ranar Talata a matsayin sabuwar ranar da zai dawo Najeriya.

Karanta Wannan  Tinubu ya amince da biliyan 16 don sake gina gadar Mokwa - Mohammed Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *