
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar bude makarantar horas da ‘Yansanda ta musamman hannu.
Makarantar me sunan Nigeria Police Training Institutes zata horas da ‘yansanda ne game da yanda zasu rika gudanar da ayyukansu daidai da zamani.
Masana sun ce wannan sabuwar makarantar ka iya zama ta farko wajan kawo gyara ga ayyukan tsaro a kasarnan