Friday, December 5
Shadow

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna, Gobe Juma’a

Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna a gobe, Juma’a idan Allah ya kaimu.

Shugaban zai halarci daurin auren dan Sanata Abdulaziz Yari me suna Nasirudeen Yari da amaryarsa, Safiyya Shehu Idris.

Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar 18 ga watan Satumba.

Hakanan sanarwar tace shugaban kasar zai kuma kaiwa matar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ziyara.

Sannan a Ranar Juma’ar dai ne shugaban zai koma Abuja.

Karanta Wannan  Yan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige shugaban majalisar, Mudashiru Obasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *