Wednesday, January 15
Shadow

Sirrin man kadanya

DAMINA UWAR ALBARKA
Wannan KADANYA kenan. Itama tana daga cikin ‘ya’yan itatuwan da ake samun wadatuwarsu a lokutan DAMINA.

Masana sun tabbatar tana dauke da:

  • Vitamins: A, C, E da kuma K
  • Minerals: potassium, magnesium da kuma iron
  • Tana dauke da Antioxidants
  • Nutritional fibre
  • Fatty acids masu Kara lafiyar jiki

A irin wannan yanayi da abincin namu sai a hankali, ya kamata mu dinga amfani da ita kuma mu bawa iyalanmu gwargwadon Hali.

Allah Ka wadace mu da lafiya, kwanciyar hankali da wadatuwar arziki a duka kasar nan tamu.

Man kadanya na taimakawa wajan hana fata tsufa da wuri.

Yana hana kaikayin fata.

Yana kare fata daga zafin rana.

Karanta Wannan  Man kadanya da Turanci

Idan ana amfani da Man kadanya yau da kullun, Yana taimakawa wajan kara Hasken Fata.

Ana iya hada man kadanya da man da ake shafawa dan karawa fata sinadari da karko.

Ana hada man kadanya da man karas dan saka hasken fata wanda bashi da illa.

Man kadanya na kawar da tabon fuska musamman me baki-baki.

Man kade na da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A da E

Wannan mai na magance kurajen fuska da gautsin fata da kuna da kuma kyasbi.

Amfani da wannan man na sanya sulbin fata.

Ga kadan daga cikin amfanin man kade.

Karanta Wannan  Gyaran nono da man kadanya

Hadin magance kyasbi:

A samu man sandal da man labender a zuba a cikin man kade sannan a kwaba su sosai sai a samu kwalba a zuba hadin.

A mayar da wannan mai man shafawa a kullum.

A yi amfani da shi na tsawon wata shida za a ga canji.

Magance fata mai gautsi:

A samu man kwakwa da man zaitun da kuma man almond sannan a zuba a kwalba a kuma zuba man kade a ciki, sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan a rika shafawa a jiki.

A mayar da man, man shafawa bayan an yi wanka.

Domin magance bushewar lebba:

A samu zuma da man zaitun sai a zuba a kan man kade a kwaba su sosai.

Sai a sa a wuri mai sanyi. Sannan a rika shafawa a baki a kullum za a samu sauki.

Karanta Wannan  Amfanin man kadanya a azzakari

Domin magance kurajen aski ga maza;

A samu man rosemary da man kwakwa sannan a zuba a kan man kade a kwaba.

A rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da suke fesowa a gemu bayan an yi aski.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *