Friday, December 5
Shadow

Sojan Najeriya da ya hana Ministan Abuja, Nyesom Wike shiga waja dake gini dan ya rusashi nata shan yabo wajan ‘yan Najeriya

Sojan Ruwan Najeriya, Lieutenant A.M. Yerima na shan yabo bayan Tirka-Tirkar da suka yi da ministan Abuja, Nyesom Wike kan sai ya shiga wajan wani gini ya hana amma sojan ya hanashi shiga.

Wike ya kira har shugaban tsaro gaba daya na kasa amma Sojan yawa Shugaban bayanin cewa na sama dashi ne ya sashi wannan aiki.

Saidai Wike ya koma yana zagin sojan da cewa, wawa ne amma sojan yace shi ba wawa bane.

Wani daga cikin yaran Wike ya gayawa sojan cewa ba zaka yi shiru ba oga na magana kana magana, Shina Wike din yace masa yayi Shiru amma yace ba zai yi shiru ba.

Karanta Wannan  Rundunar 'yansanda a Katsina ta ce ta kashe 'yanfashi 40 a 2024

Lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda da dama suka yabawa sojan.

Saidai wasu daga cikin yaran Wike sunce sojan ya sabawa ka’idar aiki inda suke cewa hakan daidai yake da yunkurin yin juyin mulki.

A yayin da Wike ke barin wajan an ji wani daga cikin tawagarsa na fadin dan Iskan Yaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *