
Janar din soja, Maj-Gen Pat Akem-Vingir (retd), ya bayyana cewa, ana bukatar karin sojoji a Najeriya muddin ana son sojojin su iya magance matsalar tsaron da ake da ita.
Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na ChannelsTV suka yi dashi inda yace a yanzu sojoji 230,000 ne Najeriya ke dasu.
Yace yawanci nasarorin da suka samu a Arewa Maso gabas akan B0K0 Hàràm an samu koma baya saboda kungiyar ta sake komawa ta kwace guraren da aka kwace daga gurinta.
Yace dan haka akwai bukatar kara yawan sojojin da ake dasu zuwa 500,000 idan ana son dawwamar da nasarar tsaro da ake samu.
Tsohon Janar din yace kuma Gwamnati ta daina kula sabuwar kungiyar masu tada kayar baya ta Lakurawa inda yace karamar kungiyace wadda za’a iya yin maganinta a lokaci guda, yace bai kamata ana maganarsu ba saboda dama auna neman sunane.