Friday, July 17
Shadow

Tabbas Akwai wata makarkashiya da munafirci a rasuwar marigayi tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha>>Inji Janar Abdulsalam Abubakar

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya da munafurci a rasuwar Janar Sani Abacha.

Ya bayyana hakane a cikin littafin rayuwarsa da ya rubuta bayan da ya cika shekaru 84 a Duniya.

Yace a lokacin da lamarin ya faru yana cikin fadar shugaban kasa, ya je ganin shugaban kasar aka ce masa shugaban yace ya jira a Falo.

Yace suna zaune shi da Janar Ishaya ba maiyi sai aka kulle kafar dakin da suke ciki ba tare da sun sani ba.

Yace ya tashi zai bude sai yaji kofar a kulle.

Yace ya tambayi janar Ishaya ko yasan da cewa an kullesu yace shima bai sani ba.

Karanta Wannan  An kama wata budurwa bayan da saurayi ya kashe mata makudan kudade amma tace ba zata aureshi ba

Yace can sai aka bude kofar, Shugaban ‘yansandan Najeriya me na wancan lokacin ya kuma sanar dasu janar Sani Abacha ya rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *