Wednesday, January 15
Shadow

Tafarnuwa na maganin infection

Infection na mata da suke fama dashi a gabansu abu ne wanda ya zama ruwan dare, a wani binciken masa na jami’ar Harvard sun bayyana cewa kaso 75 cikin 100 na mata sun taba samun ko kuma zasu samu cutar Infection a rayuwarsu.

Tafarnuwa na taimakawa sosai wajan magance matsalar cutar Infection tana hana abinda ke zama a farjin mace ya bata infection yaduwa.

Infection din gaban mata ana kiransa da Yeast infection a turance, shi Yeast din wani ruwa ne da a gaban kowace mace akwaishi, amma akan samu matsala wani lokacin sai yayi yawa sosai shine sai ya koma ya zama infection.

Ga alamomin da mace zata gane tana da cutar Infection kamar haka:

Karanta Wannan  Amfanin man zaitun da tafarnuwa

Idan kika ji gabanki na kaikai ko yana miki ba dadi.

Idan kina jin zafi yayin jima’i.

Idan farin ruwa me kauri na fita daga gabanki.

Ana amfani da Tafarnuwa wajan magance matsalar infection.

Ana iya taunata ko kuma a sakata a cikin abinci a rika ci.

Hakanan ana iya samun man tafarnuwa ko kuma a dakata a rika shafawa a gaban, amma masana aun ce kada a tura ciki.

Idan ana amfani da tafarnuwa wajan magance matsalar infection a rika lura da canjawar jiki, idan aka ga canjin da zai zama illa a dakatar a tuntubi likita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *