
Tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando mata ta Najeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon ƙwando ta mata ta Afirka.
Tawagar ta D’Tigress ta samu gagarumar tarba daga masoya ƙwallon ƙwanda a Najeriya, lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Abuja.
Ministar Mata Iman Sulaiman Ibrahim da takwararta ta al’adu, Hannatu Musawa ne suka yi wa tagawar rakiya tun daga birnin Abidjan zuwa Abuja.
A ranar Lahadi ne tawagar D’Tigress ta lashe gasar ƙwallon ƙwando ta tama ta Afirka, bayan doke Mali da ci 78-64.
Wannan ne karo na bakwai da tawagar Najeriya ta lashe kofin gasar a tarihi, wanda kuma shi ne na biyar a jere da ta ɗauka.