
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata cika Alkawuran data daukarwa ‘yan Najeriya ba.
Yace dan haka bata cancanci a sake zabenta ba.
Ya bayyana hakane bayan komawar wasu ‘yan PDP jam’iyyar APC inda yace ko a jikinsa.
Hakanan Atiku yace masu sukarsa game da ziyara da ya kaiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari munafukaine.
Yace Buhari tsohon shugaban kasa ne kuma me ruwa da tsaki a siyasar Najeriya.
Yace a lokacin da ya rika kaiwa Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ba’a rika zaginsa ba sai da ya ziyarci Buhari.