
Gwamnan jhar Anambra, Charles Soludo ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tseratar da Najeriya daga fadawa kangin Talauci.
Ya bayyana hakane a cikin jawabinsa na ranar ‘yanci inda yace tsare-tsaren tayar da komar tattalin arziki na gwamnatin shugaban kasar na aiki yanda ya kamata.
Yace tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya dauki saiti kuma za’a iya ganin tabbacin hakan ta hanyar yabo da shugaban kasar ke samu daga hukumomin Duniya irin su IMF da bankin Duniya da sauransu.
Soludo yayi kira ga jam’iyyun Siyasa da su hada kai a muradi na bai daya na ci gaban kasa.