
Matashin Mawaki Bilal Villa Ya Sha Ruwan Duwatsu A Kaduna A Yayin Wasan Sallah, Inda Aka Farfasa Masa Mota, Yayin Da Shi Ma Takwaransa, Ngulde Ya Hadu Da Fushin Katsinawa Inda Suka Rotse Masa Kai Da Dutśe A Yayin Wasan Sallah
A yayin da ba a san dalilin da ya sa aka fatatti Bilal Villa a Kaduna ba, amma wata majiya ta gano cewa shi Ngulde ya tabo Katsinawa ne, inda a wata ziyarar da ya kai Katisna, yana sauka sai ya bankawa sigari wuta, wanda hakan yana nufin al’adar su ce shan sigari.