
Kungiyar Dattawan Arewa, NEF ta mayarwa da shugaban kasar Amirka, Donald Trump da martani me zafi inda tace shugaban Amurkar, Trump bai isa ya hana aiki da Shari’ar Musulunci a Jihohin arewa ba
Wasu daga cikin ‘yan majalisar kasar Amurka da wasu kungiyoyin fafutuka a kasar sun nuna damuwa kan amfani da shari’ar Musulunci a jihohin Arewa.
Dan haka suke kiran a daina amfani da shari’ar Musulunci a Arewa sannan a sakawa wasu jami’an gwamnatin Najeriya takunkumi.
Saidai kungiyar NEF ta bakin me magana da yawunta, Prof Abubakar Jiddere tace babu wannan maganar, Trump girman kai ne ke Damunsa kuma barzanar da yake yi ta banza da wofi ce babu abinda zai iya.
Sannan kungiyar tace babu maganar yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi a Arewa matsalar tsaro tana shafar kowa da kowane.
Hakanan itama gamayyar Kungiyoyin fafutuka na arewa, The National Coordinator of the Coalition of Northern Groups ta bakin shugabanta, Jamilu Aliyu Charanchi, tace wannan abu zai karawa mutane tsanar kasashen yamma ne kawai.
Yace Shari’ar Musulunci ba wai doka bace kawai, abune wanda ‘yan Arewa musulmi suka yadda cewa daga Allah ne kuma haka rayuwarsu ya kamata ta kasance.
Yayi gargadin cewa, duk Gwamnan da ya sake yayi yunkurin sassautawa ko cire shari’ar Musulunci to zai fuskanci kakkausan Martani daga Al’ummar Arewa da malamai.