
Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, zai tsaya neman takarar sanata na kujerar da Sanata Natasha Akpoti ke kai.
Ya bayyana hakane a fadar sarkin Ohinoyi dake Okene ranar 29 ga watan Disamba.
Hakan ya kawo karshen rade-radin da ake kan cewa ko zai tsaya takarar ko kuwa.
Yahya Bello dai na da case a EFCC inda suke Tuhumarsa kan zargin cinye wasu kudade har Biliyan 80 na jiharsa.