
Sun shirya wannan tafiya ce domin yabon gwani ya zama dole. Domin a cewar su kowa ya san yadda Alhaji lbrahim Kabir Masari yake kokari sosai da kuma jarincewa wajen alki da nuna kishin yankinshi. Dan haka a matsayinmu na Katsinawa za mu zo mu gaida shi kuma muna son ganin shi idon da ido.
Kuma a matsayinshi na ubanmu shi zai kai mu wajen shugaban ‘yan sanda na kasa bisa kokari da hukumar ‘yan sanda ke yi domin dada tsaro ga a’lummar kasa bakin daya. Wanda bisa haka ne muka yanke shawara gani IGP na kasa don mu yaba masa.
Daga Shi ma IG ya kai mu wajen tsuhuwar Ministar ‘yan sanda bisa namiji kokari da ta yi wajen nuna kishi da kuma taimako da ta yi wa kasa, musamman fanninmu Katsina ta bada waje domin tallafawa matan ‘yan sanda da suka rasu. Da kuma taya ta murnar samu wani matsayi na ministar Jin kan mata.
Sai kuma matan makaimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima bisa kokari da yakewa al’umma ita da mijinta, wanda kowa ya san yanzu Arewa sanadiyar mijinta ana jin dadi.
Matasan sun taso ne daga karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina.
Domin karin bayani za a iya samun su a wannan lambar; 07049144068