
Shahararriyar Wada wadda suka rika sheke aya tare da Idris Mai Wushirya ta bayyana cewa ta ga an daina mata likes da comment da kallon Bidiyon da take wallafawa.
Tace tana nema dan darajar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a dawo a ci gaba da yi mata.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyon ta da ya watsu sosai kuma hakan na zuwane bayan da aka kama abokin burmin nata watau mai wushirya inda yake can a tsare.