
Wani Bidiyo da aka dauka na fadar shugaban kasa, Villa, ya dauki hankula.
Bidiyon an daukeshi ne da jirgi marar Matuki ta sama wanda ya nuna kowane sashe na fadar shugaban kasar dake Abuja.
Bidiyon ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga mutane na ta Allah wadai da fadar cewa bai kamata a bari wani ya dauki irin wannan Bidiyon ya yadashi a kafafen sada zumunta ba.
Wasu na kafa Misalai da cewa, a kasashen Duniya da suka ci gaba har ma dana Afrika ba za’a bari irin haka ta faru ba.