
Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya buga masa a ka Ya rasu.
Cikin wani sako da mai magana da yawun randunar SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa yace “Matashi yaje zance wajen budurwa, yayanta ya fito da gora ya buga masa a ka. Ya rasu, shi kuma yana hannun Yan Sanda.
Daga karshe Kiyawa yace nan gaba kadan zasu fitar da cikakken bayani.