
Wani me laifi me suna Benjamin Schreiber da ake tsare dashi a gidan yari na jihar Iowa dake kasar Amurka saboda aikata kisa aka kuma mai hukuncin daurin rai da rai yace a sakeshi yanzu ya gama zaman gidan yarinsa tunda ya mutu ya dawo.
Wata Kwaya ce ya sha ta sa yayi Doguwar suma shine da ya farfado ya shigar da kara yace wai a sakeshi tunda ya mutu ya dawo.
Alkali dai yayi watsi da wannan bukatar tashi inda yace har yanzu yana nan da ranshi be mutu ba.