Friday, December 5
Shadow

Wani Tsohon Janar yace Tun zamanin Buhari an kama wasu dake da hannu a matsalar tsaron Najeriya wanda ke da alaka da Janar Tukur Yusuf Buratai, da Abubakar Malami, da Godswin Emefiele da tsohon shugaban sojoji Gen. Faruk Yahaya (rtd) 

Sahara Reporters ta ruwaito cewa, wani tsohon janar, General, Ali-Keffi ya bayyana cewa a zamanin tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari an nadashi ya jagoranci binciken masu daukar nauyin ‘yan ta’adda a Najeriya.

Yace binciken su ya kamo mutane 20 da ake zargi.

Yace cikin mutane 20 din da ake zargi akwai wadanda ke da alaka da Tsohon shugaban sojoji, Janar Tukur Yusuf Buratai da Tsohon babban lauyan Gwamnati, Abubakar Malami da Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele da tsohon shugaban sojoji, Janar Farouk Yahya.

Yace amma kwatsam sai aka kamashi.

Yace ana tsareshi na wani lokaci sannan aka masa ritayar dole.

Karanta Wannan  Zamu daina baka makamai da yanke duk wata hulda da kai idan ka ci gaba da Kàshè Palasdiynawa>>Shugaba Trump ya gargadi Firaiministan Israyla, Benjamin Netanyahu

Yace har yau bai san laifin da ya aikata ba aka masa wancan wulakanci.

Yace sannan ya samu Labarin an saki mutane 20 din da suka kama inda aka gargadesu cewa kada su sake su yi hira da manema labarai sannan kada su ce zasu je kotu dan neman hakkinsu kan kamen da aka musu.

!Yace kuma manyan mutanen da aka samu da alaka da wadannan mutanen ba wai yace yana zarginsu da daukar nauyin ta’addanci ba amma bai san ko an bincikesu ba ko kuwa an rufe maganar ne gaba dayanta?.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *