Saturday, March 15
Shadow

Wasu bala’o’i sun aukawa kasar Amurka inda A birnin Los Angeles aka yi girgizar kasa, a South Carolina gobarar daji ce ta kunno kai

An samu girgizar kasa me maki 3.9 a birnin Los Angeles na Jihar California ta kasar Amurka.

Hakan na zuwane bayan da aka kammala bikin bayar da kyautar Oscar 2025.

Gurare da yawa da suka hada da Pasadena, Long Beach, San Fernando Valley, Torrance, Redondo Beach da Glendale sun bayyana cewa sun ji motsin kasa.

Babu dai rahoton cewa wani ya ji rauni.

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da aka samu mummunar gobarar daji a birnin na Los Angeles.

Hakanan a jihohin South Carolina da North Carolina na kasar Amurkar ma Wutar daji ce ta barke inda ake maganar taci kadada sama da 1,600 a South Carolina inda a North Carolina kuma taci kadada sama da 500.

Karanta Wannan  Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Mahukunta a yankunan da gobarar ta tashi sun bayar da umarnin mutane su fice daga yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *