Wednesday, March 25
Shadow

Wata mata wadda tace ita ‘yar Kwangila ce, tace ta kaiwa Ministan Ayyuka, David Umahi kayan aiki na Naira Miliyan 304 Shekaru 12 da suka gabata amma yaki biyanta

Wata mata me suna Tracy Nicolas Ohiri ta bayyana inda ta zargi Ministan ayyuka, David Umahi da kin biyanta kudin kayan aiki data kai masa.

Matar tace ta kaiwa Ministan kayan aiki na Naira Miliyan 304 tun shekaru 12 da suka gabata amma yaki biyanta kudin.

A jawabin da takewa manema labarai ta zargi Ministan da neman ta su yi soyayya amma tace masa a’a domin ita matar aurece.

Tace tana da chat din da suka yi da kum irin maganganun da ya rika gaya mata wanda basu dace ba.

Matar dai ta fito ta gayawa Duniya inda hakan yasa aka tura ‘yansanda su kamata daga legas zuwa Abuja aka tsareta

Karanta Wannan  PDP ta koka da cewa, APC na ta mata kwacen mutanenta inda a yanzu haka Gwamnonin da suka rage ana musu Alkawari me gwabi idan suka shiga APC

Dan Fafutuka, Omoyele Sowore ya shiga lamarin inda a zaman da aka yi da matar da ‘yansanda da David Umahi, Ministan yace be san matar ba inda ta tayar da bori.

Saidai da Omoyele Sowore suka shiga dakin taron sau aka tashi, an ga Sowore ta tare Ministan inda yake gaya masa cewa ya daina amfani da ‘yansanda yana fada akan abinda ya shafi rayuwarsa shi kadai.

Karanta Wannan  Gidana na Alfarma da ake ta cece-kuce akai na ginashi ne tun kamin in zama Minista>>Inji Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *