Sunday, August 16
Shadow

Wata mata wadda tace ita ‘yar Kwangila ce, tace ta kaiwa Ministan Ayyuka, David Umahi kayan aiki na Naira Miliyan 304 Shekaru 12 da suka gabata amma yaki biyanta

Wata mata me suna Tracy Nicolas Ohiri ta bayyana inda ta zargi Ministan ayyuka, David Umahi da kin biyanta kudin kayan aiki data kai masa.

Matar tace ta kaiwa Ministan kayan aiki na Naira Miliyan 304 tun shekaru 12 da suka gabata amma yaki biyanta kudin.

A jawabin da takewa manema labarai ta zargi Ministan da neman ta su yi soyayya amma tace masa a’a domin ita matar aurece.

Tace tana da chat din da suka yi da kum irin maganganun da ya rika gaya mata wanda basu dace ba.

Matar dai ta fito ta gayawa Duniya inda hakan yasa aka tura ‘yansanda su kamata daga legas zuwa Abuja aka tsareta

Karanta Wannan  Idan ba Gwamnatice ta daure mana Gìndy muke abìndà muke ba Allah ya Tsynè min Allbarka>>Inji Wani Tshàgyèràn Dhàjì

Dan Fafutuka, Omoyele Sowore ya shiga lamarin inda a zaman da aka yi da matar da ‘yansanda da David Umahi, Ministan yace be san matar ba inda ta tayar da bori.

Saidai da Omoyele Sowore suka shiga dakin taron sau aka tashi, an ga Sowore ta tare Ministan inda yake gaya masa cewa ya daina amfani da ‘yansanda yana fada akan abinda ya shafi rayuwarsa shi kadai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda Wasu limaman kirista ke durkusawa suna sumbatar wani gicciyayyen Gunki ya dauki, Hankula, Har wasu kiristocin sun ce abin ya basu kunya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *