Tuesday, February 3
Shadow

Wata Sabuwa: An gano Wani babban Janar na da hannu a yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Rahotanni daga jaridar Premium Times sun bayyana cewa, an gano wani janar na da hannu a yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu jhuyin Mulki.

Janar din sunansa Adamu, kuma yayi ritaya daga aikin soja, saidai zuwa yanzu shi ba’a kamashi ba.

Hakanan akwai karin wasu da ake zargi da hannu a lamarin Jhuyin mulkin wanda suma ba’a kamasu ba.

Jaridar ta Premium Times tace wasu jami’an tsaro dake kusa da inda ake wannan abincike sun bayyana cewa, wanda suka shirya Jhuyin mulkin sun sayi motoci kusan 32 wanda zasu yi amfani dasu dan basaja wajan aikata wannan laifi.

An samu tabbas na rasit sa aka sayi motocin da sauran bayanai da suka tabbatar da hakan.

Karanta Wannan  Karanta Jadawalin jami'o'in Najeriya dake bada Admission da makin Jamb 140, 150, da 160

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *