Wednesday, January 15
Shadow

WATA SABUWA: Babbar Kotu a Najeriya ta hana dukkan jami’an tsaron Najeriya kora ko fitar da Sarki Sanusi Lamido Sanusi II daga Fadar Sarki

Wata babbar kotu a Kano ƙarkashin jagorancin mai shari’a Amina Aliyu ta hana ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS da sojojin Najeriya daga korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ko fitar dashi daga fadar Sarki.

Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Sarkin ne ya shigar da ƙara tare da majalisar masu naɗin sarakunan Kano su hudu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan da; Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.

Menene ra’ayinku kan wannan turka-turka na sarautar Kano?

Karanta Wannan  Da Duminsa: EFCC ta gayyaci Kwankwaso zata fara bincikenshi kan Naira Biliyan 2.5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *