
Mijin Hussaina Seaman Abbas yayi Jawabi yace babu abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa Hussaina.
Ya bayyana hakane bayan da bidiyon ta ya bayyana aka ji tana cewa yanzu basa tare kuma tana musanta cewa an bata kudi da mota.
Seaman Abbas ya karyata cewa akwai matsalar kudi data taso tsakaninsu. Kalli Bidiyon nasa anan
Bidiyon da Husaina ta yi dai bai yiwa Ordinary President dadi ba inda ya bayyana cewa itama ta yadda da zargin da ake cewa an bashi kudi ya ki bata kenan. Kalli bidiyon hussaina nan
A bidiyonsa da yayi magana kan lamarin a wajan shirya shirin da yake yi, ya bayyana cewa, shine ya rika kashe kudi akan case din Husaina amma babu wanda ya bashi ko sisi. Kalli bidiyon anan