Wednesday, January 15
Shadow

WATA SABUWA: Saura kaɗan mu kama Bello Turji – Janar Chris Musa

Babban hafsan tasro na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ci alwashin kama ƙásurgųmi kuma jagorán ‘yaɲ fáshíɲ daji Bello Turji “nan ba da jimawa ba”.

BBC ta rawaito Musa yana magana yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, janar ɗin ya ce: “Saura kaɗan mu kama Turji.”

Game da wa’adin biyan kuɗin haraji da aka ce Turji ya bai wa mazauna yankunan jihar Zamfara, Janar Musa ya ce sojoji na aiki da sauran hukumomin tsaro domin kare mazauna yankunan.

“Game da Turji, mutum ne kawai da ya sauka daga kan layi kuma yake tunanin ya isa, amma ina tabbatar muku za mu kamo shi kuma cikin ƙanƙanin lokaci,” in ji shi.

Karanta Wannan  Ka Yi Gaggawar Janye Kalamanka Kan Dokar Haraji Domin Zai Tada Hankulan 'Yan Kasa, Umarnin Fadar Shugaban Kasa Ga Gwamnan Bauchi

Shugaban sojojin ya kuma nemi mazauna yankunan da su bai wa sojoji haɗin kai.

“Kada ku taimaka musu, kada ku ba su wasu bayanai game da samamen da muke kaiwa saboda abin da yake faruwa yanzu kenan.”

Shin kuna ganin cewa ya kamata a riƙa bayyanawa duniya idan za’a yi irin wannan sumamen ?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *