Thursday, March 5
Shadow

Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, me martaba sarkin  Kano, Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a jihar Kaduna.

Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter.

Sani yace Sarki Muhammad Sanusi II yana yakar zalunci a jihar  Kano amma kuma a baya ya goyi bayan zaluncin a jihar Kaduna.

Sarki Sanusi dai abokine a wajan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma a lokacin da aka cireshi daga mukamin sarkin Kano, ya koma Kaduna inda El-Rufai ya bashi waje ya bude fada sannan kuma ya bashi mukami a jami’ar jihar Kaduna.

Karanta Wannan  Dole Sabon fafaroman da za'a zaba kada ya yi irin abinda marigayi Fafaroma Francis yayi na goyon bayan 'yan Luwadi da Madigo, Baibul ya koya aure tsakanin namiji da mace ne kawai>>Inji Wani babban Limamin Kirista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *