Tauraron Fina-finan Hausa kuma mawaki, Sani Musa Danja ya bayyana cewa, Tsohon sarkin Kano da majalisar jihar Kano ta sauke, Aminu Ado Bayero ya hakura ya ajiye lema da sanda ya tafi amma wasu suka zigoshi ya dawo.
Sani Musa Danja ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya saka a shafinsa na sada zumunta inda ya yi tsokaci akan rikicin siyasar Kano.
Yace abin takaici shine duka sarakan ‘yan uwan junane amma an dauko wani abu da zai saka gaba da kiyayya a tsakaninsu.
Sani Musa Danja yayi kiran kawo abinda zai sa zaman lafiya da ci gaba ya dare a Kano.