Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna rashin jin dadinsa kan sauke Aminu Ado Bayero da Gwamnatin jihar Kano ta yi.
A jawabin da ya fitar ta bakin kakakinsa, malamin yace yana baiwa majalisar tarayya shawara ta yi dokar da zata hana ‘yan siyasa saukewa da wulakanta sarakai.
Gwamnatin jihar Kano, Karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero inda ta mayar da Sarki Muhammad Sanusi II akan kujerar.
Lamarin ya jawo tashin hankula a jihar ta Kano inda Sarki Aminu Ado Bayero ya dawo yake ikirarin cewa shima sarkine.