Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake amfani da tsinken gwajin ciki

Tsinken Gwajin ciki na bayar da sakamako me kyau idan aka yi amfani dashi yanda ya kamata.

Saidai kamin a yi amfani dashi, masana sun ce ya kamata a bari sai bayan kwnaki 10 banyan yin jima’i, ko kuma idan ana son sakamako wanda yafi kyau a bari sai bayan kwanaki 14, wasu ma sun ce kamata yayi a bari sai bayan kwanaki 21 da yin jima’i yayin da wasu suka ce a bari sai idan ba’a ga jinin al’ada ba.

Shawara anan itace, idan kin kagara ki ga sakamakon kina iya yin gwajin a duka lokutan guda 3 ko hudu, watau ki yi bayan kwanaki 10 da bayan kwanaki 14 da bayan kwanaki 21 da kuma bayan baki ga jinin al’ada ba.

Karanta Wannan  Gwajin ciki na sati daya

Yanda ake amfani da tsinken gwajin ciki shine, Ana samin kofi ko mazubi sai a yi fitsari a ciki, sai a saka rabin tsinken a cikin fitsarin.

Sai ki fiddoshi ki ajiyeshi a kwance zuwa mintina 1 zuwa 5.

Bayan nan zaki ga sakamako:

Idan ya nuna layi guda biyu ko da layin na biyu yayi dishi-dishi be fito da kyauta, to babu tantama kina da ciki.

Idan kuma ya nuna layi daya to baki da ciki.

Abubuwan da za’a kiyaye dan samun sakamako me kyau:

Ki yi amfani da fitsarinki na farko da safe bayan kin tashi bacci.

Kada a sha ruwa ko wani abu kamin a yi gwajin.

Karanta Wannan  Yadda mai ciki zata kwanta

Ki tabbatar lokacin lalacewar tsinken gwajin cikin bai yi ba, watau ki duba jikin kwalin ko takardar ana rubuta ranar da zai lalace, ki tabbatar ranar bata yi ba, idan kuma ta yi, watau ya lalace, abinda ake cewa expiring date, to sai a sayi wani ko kuma a mayar a canja.

Masana sunce gwajin ciki na fitsari da tsinken fitsari idan an yishi yanda ya kamata shine yafi bada sakamako me kyau.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *